WASHINGTON, D.C. - A bayanin nata, Selene Gomez ta godewa Rema da ya zabe ta suka yi waka tare, a wani jerin wakokin da ake dauka a matsayin daya daga cikin manyan jerin wakoki a duniya, ta kuma ce ya canza rayuwarta har abada.
Mawakiyar ta kuma dora hotuna guda biyu da suka dauka tare da Rema akan shafin ta, sannan ta rubuta cewa, “Wannan mutumin ya canza rayuwata har abada. Rema, na gode da ka zabe ni muka yi daya daga cikin manyan wakoki a duniya. Ina kaunar ka har abada.”
Tuni mutane suka fara maida martani, inda a cikin kwana guda da kafa hoton na su da Salena ta yi, sama da mutane miliyan bakwai suka yaba, yayinda da dama suka yaba hadin guiwar tsakanin matasan mawakan.
Rema mai shakaru 23 a duniya ya mayar da martani ga sakon na Gomez, inda ya bayyana tasa kaunar a gare ta a kan shafin na Instagram, yana mai cewa, “ni ma ina kaunar ki Sarauniya ta."
An haifi shahararran mawakin wanda ya sami lambobin yabo da yawa, wanda ainihin sunansa Divine Ikubor ne, amma aka fi sanin shi da Rema, ranar 1 ga Mayu 2000.