Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Murna Ta Koma Cikin Ga Fatan ‘Yan Najeriya Na Magance Matsalar Tsaro


Shugaban Kasar Najeriya Bola Ahmed Tinubu
Shugaban Kasar Najeriya Bola Ahmed Tinubu

Fatar da ‘yan Najeriya ke da ita ta magance matsalar rashin tsaro a karkashin sabbin gwamnatoci, na ci gaba da dushewa  saboda yadda ‘yan bindiga ke zafafa kai hare-hare daidai lokacin da sabbin gwamnatoci ke kusa da cika kwana arba'in kan mulki.

SOKOTO, NIGERIA - Yankuna da dama ne har yanzu ke fuskantar hare-haren ‘yan bindiga a Arewacin Najeriya, bayan jan ragamar shugabanci da sabbin shugabanni suka yi.

Al'ummomi dake wasu yankuna sun fi shan ukubar ‘yan bindiga saboda yanayin wuraren da suke zaune yana da saukin shiga ga ‘yan bindigar su aikata ta'asar su. Kamar yankin kudancin jihar Kebbi dake Arewa maso Yammacin Najeriya, da yankin Wasagu, Wari ne da ya yi iyaka da dazukan da ke jihohin Neja da Zamfara, dazukan da suka yi kaurin suna da ayyukan ‘yan bindiga.

Wani mutumin Wasagu, Shehu A Raba Hasara ya ce jama'ar yankin kullum ba su barci da ido biyu rufe saboda fargabar harin ‘yan bindiga domin a kullum sai sun shigo sun dauke mutane, har ta kai ga barayin sun aikawa mutanen cewa duk lokacin da suka bukaci kudi, to Wasagu zasu shiga.

A jihar Sakkwato ma yankunan gabashin jihar sune ko da yaushe cikin damuwa.

‘Dan majalisar jiha na Isa, Habibu Halilu Modaci ya ce Isa da Sabon Birni da Shinkafi yanzu suna cikin mawuyacin hali saboda yadda ‘yan bindiga ke farautar jama'a tamkar zomaye, musamman idan sun je gona, wasu lokuta su sace mutane wasu lokutan kuma su kashe su.

A wata ziyara da mataimakin gwamnan jihar Kebbi Sanata Abubakar Umar Tafida ya kai a yankin Kudancin jihar ya bayar da tabbacin shirin sabuwar gwamnatin Dokta Nasir Idris wajen shawo kan matsalar.

Yanzu kusan kwana arba'in da soma mulkin sabbin gwamnatoci, duk da yake sun yi alkawura na kokarin samar da tsaro, amma har yanzu ba abinda ya canja daga yadda ake a lokacin gwamnatocin da suka ajiye mulki a watan Mayun da ta gabata.

Dr. Yahuza Ahmad Getso masani akan harkokin tsaro a Najeriya ya ce sabbin gwamnatoci suna iya kokarin su don dakile matsalar, gwamnatin Najeriya ma acewar ta, ba ta da isassun makamai da jami'ai isassu da zasu iya dakile matsalar a duk fadin Najeriya.

Haka kuma ya ce akwai matsalar rashin samun hadin kai tsakanin jama'a da jami'an tsaro da dai wasu matsaloli da dole sai an kawar da su za'a iya samun nasara.

Yanzu dai al'ummomi dake fama da wadannan matsalolin da ma wadanda ba su ciki na kyautata fatar samun mafita domin samun wanzuwar zaman lafiya da ci gaban kasa.

Saurari cikakken rahoton Muhammad Nasir:

Murna Ta Koma Cikin Ga Fatan ‘Yan Najeriya Akan Magance Matsalar Tsaro .MP3
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:26 0:00

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG