Gwamnatin Najeriya ta bayar da umarnin mayar da hedikwatar hukumar kula da sufurin jiragen sama ta kasa FAAN daga babban birnin tarayyar kasar Abuja zuwa Legas.
An shiga rana ta biyu ta tarzomar da ta tashi a tsibirin Comoros da ke tsakiyar tekun Indiya a yau Alhamis wanda ya yi sanadin mutuwar mutum guda tare da jikkata wasu akalla shida, in ji wani jami’in lafiya.
Kasar Zambia na fama da barkewar cutar kwalara da ta kashe mutane sama da 400 kuma wasu fiye da10,000 sun kamu da cutar, lamarin da ya sa hukumomi suka ba da umarnin rufe makarantu a fadin kasar bayan hutun karshen shekara.
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya fada ranar Talata cewa gwamnatinsa za ta fara "gagarumin shirin ilimantarwa" ga matasa a matsayin daya daga cikin hanyoyin magance karuwar satar mutane don neman kudin fansa da ke barazana ga babban birnin kasar tare da yankunan Arewacin kasar da ke fama da rikici.
Hukumar ba da agajin gaggawa ta Najeriya ta sanar a jiya Talata cewa fasinjoji takwas ne aka tabbatar sun mutu, sannan kimanin wasu 100 kuma sun bace, bayan kifewar kwale-kwalen da suke ciki a arewa maso tsakiyar kasar.
Kamfanin Shell ya fada a ranar Talata cewa ya cimma matsayar sayar da kasuwancinsa na teku a yankin Niger Delta na Najeriya ga wata hadakar kamfanoni, a wata yarjejeniya da ta kai dala biliyan 2.4.
Uwargidan shugaban kasar Najeriya Remi Tinubu, ta bi sahun jama'ar da suka yi tir da Allah wadai da kisan wata daliba da aka sace tare da wasu 'yan uwanta mata guda biyar, inda ta bayyana hakan a matsayin "mummunan rashi".
Matatar man fetur mafi girma a nahiyar Afirka ta fara aiki a Najeriya, kamar yadda kamfanin ya bayyana, wanda ya kawo karshen tsawon shekaru da aka kwashe ana jiran soma aikin masana'antar.
A ranar Lahadi ne mataimakin shugaban kasar Najeriya Kashim Shettima ya bar Abuja domin halartar taron shekara-shekara na dandalin tattalin arzikin duniya a Davos na kasar Switzerland da za a gudanar daga ranar 15 zuwa 19 ga watan Janairu, 2024.
Amurka ta dauki batun harkokin lafiyar da muhimmanci a matsayin abinda ya shafi tsaron kasa a cikin 2024.
Afirka ta Kudu ta ce fiye da kasashe 50 ne suka nuna goyon bayansu ga shari'ar da ta gabatar a babbar kotun Majalisar Dinkin Duniya da ke zargin Isra'ila da kisan kare dangi a kan Falasdinawa a yakin Gaza.
Sojojin Amurka da na Birtaniyya sun yi ruwan bama-bamai kan 'yan Houthis da ke samun goyon bayan Iran a Yemen a ranar Alhamis, a wani gagarumin harin ramuwar gayya ta hanyar amfani da makamai masu linzami da jiragen yaki na Tomahawk da jirgin ruwan yaki da na karkashin ruwa, in ji jami'an Amurka.
Domin Kari