WASHINGTON, D. C. - Zanga-zangar dai ta auku ne bayan da aka ayyana shugaba mai ci Azali Assoumani a matsayin wanda ya lashe zaben da aka gudanar a karshen mako wanda jam'iyyun adawar kasar suka yi tir da cewa, an yi magudi.
Sanarwar da aka yi a yammacin ranar Talata cewa, Assoumani ya lashe wa'adi na hudu ya haifar da kazamin zanga-zangar da aka fara ranar Laraba, inda aka kona gidan wani ministan gwamnati yayinda aka kona wata mota a gidan wani ministan.
Haka kuma mutane sun lalata ma'ajiyar abinci ta kasa. An toshe hanyoyi da dama a ciki da wajen babban birnin kasar, Moroni, inda masu zanga-zangar suka kafa shinge, suka kuma kona tayoyi. 'Yan sandan kwantar da tarzoma sun yi arangama da masu zanga-zangar.
Lamarin da ya sa Gwamnatin kasar ta ba da umarnin sanya dokar hana fita a daren Laraba, har zuwa karfe 6 na safiyar Alhamis.
Mutumin da ya rasu matashi ne, in ji Dr. Djabir Ibrahim, shugaban sashen bayar da agajin gaggawa na asibitin El-Maaruf da ke Moroni. Ya ce mai yiwuwa mutumin ya mutu ne sakamakon harbin bindiga. Daya daga cikin wadanda suka jikkata na cikin mummunan yanayi, in ji shi.
Babban jami'in kare hakkin bil'adama na Majalisar Dinkin Duniya, Volker Türk, ya yi kira da a kwantar da hankula, ya kuma bukaci hukumomi da su bar mutane su yi zanga-zanga cikin lumana. Ofishinsa ya ce ya samu rahoton cewa jami’an tsaro sun harba hayaki mai sa hawaye kan masu zanga-zangar lumana, ciki har da tattakin da wasu mata suka yi a farkon makon nan.
Turk ya kuma ce ya damu da sha’anin danniya a Comoros a cikin 'yan shekarun nan.
-AP
Dandalin Mu Tattauna