Masar na shirin shirya wani yanki a kan iyakar Gaza wanda zai iya daukar Falasdinawa idan har hare-haren Isra'ila a kan Rafah ya yi sanadin 'yan gudun hijirar zuwa kan iyaka, in ji majiyoyi hudu, a wani mataki da suka bayyana a matsayin wani yunkuri na gaggawa da birnin Alkahira ke shiryawa.
Wata mata mai ‘ya’ya biyu ta mutu sanan mutane 21, ciki har da akalla yara takwas, sun raunata a yayin wani harin bindiga da ya auku a wani tashar jirgin kasa mai tarihi da ke birnin na Kansas a Jihar Missouri.
Wasu gungun 'yan tawaye sun kai harin bam a wani sansanin 'yan gudun hijira da ke lardin Kivu ta Arewa da ke gabashin Congo inda suka kashe fararen hula uku tare da jikkata wasu takwas, a cewar wata kungiyar fararen hula a jiya Talata.
Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan a ranar Laraba ya kai ziyararsa ta farko a Masar tun shekara ta 2012, inda ya gana da Shugaba Abdel Fattah al-Sisi
An sako wata Likita ‘yar kasar Poland da aka yi garkuwa da ita a Chadi kuma tana cikin "koshashiyar lafiya," in ji ministan harkokin wajen Poland a ranar Talata.
An sake kama wani mutum da ake nema ruwa a jallo a jihar Massachusetts domin fuskantar tuhumar kisan kai, mako guda bayan ya tsere da dubara daga hannun ‘yan sanda, in ji ‘yan sandan Kenya a ranar Laraba.
Isra'ila da Hamas na ci gaba da tattaunawa kan samun yarjejeniyar da ke da nufin samun tsagaita wuta da kuma 'yantar da mutanen da aka yi garkuwa da su a zirin Gaza, a cewar jami'ai biyu da ke da masaniya kai tsaye kan tattaunawar.
Farashin hannun jari Access Holdings na Najeriya ya fadi da kaso 6.26 a yau yayin da masu hannun jari a kamfanin ke alhinin rasuwar Herbert Wigwe.
'Yan sanda a Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango sun harba barkonon tsohuwa a ranar Litinin don tarwatsa masu zanga-zangar da suka kona tayoyi da tutocin Amurka da na Belgium a kusa da ofisoshin jakadancin kasashen Yamma da na MDD a birnin Kinshasa don nuna fushinsu kan rashin tsaro a gabashin kasar.
Ana ci gaba da neman wata likita ‘yar kasar Poland da aka yi garkuwa da ita a kudancin kasar Chadi, kamar yadda jami'ai da kafafen yada labarai a kasar Poland suka ruwaito yau Litinin.
Jami’an hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta Najeriya wato NDLEA sun kama wani mutum mai shekaru 42 da aka ce yana jigilar dubunnan miyagun kwayoyin na Opiod a boye zuwa wani yanki na ‘yan tada kayar baya a yankin Banki na jihar Borno.
Mun ji ta bakin wasu a jihar Kano inda masu kasuwancin gurasa suka yi zanga-zanga a kan tsadar kaya a Najeriya; Yayin da kasashen Afirka ke ci gaba da fafatawa a gasar AFCON, wata karamar gasar ta kwaikwayon AFCON ta na gudana a birnin Jos na Najeriya, da wasu rahotanni
Domin Kari