Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ranar Mata Ta Duniya (IWD)


IWD - Ranar Mata Ta Duniya
IWD - Ranar Mata Ta Duniya

IWD rana ce ta musamman da aka kebe a duniya domin bikin murnar nasarorin zamantakewa, tattalin arziki, al'adu, da siyasa na mata.

WASHINGTON, D. C. - Ranar ce kuma da ake kira a duniya na neman haɓaka daidaiton jinsi. Ana ganin gagarumin ayyuka a duk fadin duniya yadda ƙungiyoyi ke taruwa don nuna murnar nasarorin da mata suka samu ko gangamin neman daidaito wa mata.

IWD - Ranar Mata Ta Duniya
IWD - Ranar Mata Ta Duniya

Ranar ce wadda aka kebe a kowace shekara 8 ga watan Maris, kuma IWD yana ɗaya daga cikin mahimman ranaku a ko wacce shekara ya zuwa yanzu:

* murnar nasarori da mata suka samu

* ilimantar da wayar da kan mata game da daidaiton mata

* kira akan neman sauyi ko canji mai kyau don samun ci gaban mata

* samun shiga don haɓaka daidaiton jinsi

* tara kudade ga kungiyoyin agaji da suka mayar da hankali ga mata women-focused charities

IWD
IWD

Taken IWD na wannan shekara ta 2024 shi ne Inspire Inclusion.

Wato ku yi tunanin duniya da ba marabar jinsi. Duniya mara son zuciya, ra'ayi, da wariya. Duniya mara banbance-banbance, daidaitacce, da kuma haɗa kai. Duniyar da ke da daraja da kuma girmama kowa. Tare za mu iya samar da daidaito ga mata. Gaba ɗaya zamu iya dukan mu #InspireInclusion.

IWD
IWD

Don haka ku yi murnar nasarar mata. Ku daga murya wajen hana wariya, ku wayar da kan jama'a game da wariya. Ɗauki Matakai don samun daidaiton jinsi.

IWD na kowa ne, a ko'ina. Hadawa yana nufin duk aikin IWD yana aiki.

-IWD

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG