WASHINGTON, D. C. - Jirgin LATAM Airlines LA800, Boeing 787-9 Dreamliner, ya sauka a filin jirgin saman Auckland kamar yadda aka shirya a ranar Litinin da yamma, a cewar FlightAware. Jirgin ya saba tsayawa a Auckland akan hanyarsa ta zuwa Santiago, Chile ne.
Wani mai magana da yawun kamfanin jirgin na Kudancin Amurka wato American Airline ya shaidawa jaridar Herald cewa an samu "matsalar fasaha" a cikin jirgin da ya shafi wasu ma'aikata da fasinjoji, ba tare da bayar da karin bayani ba.
Motar daukar marasa lafiya ta Hato Hone St. John ta yi wa mutane kusan 50 jinya a filin jirgin, kamar yadda mai magana da yawun ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters. Majinyaci ɗaya yana cikin wani mummunan yanayi, kuma sauran sun sami raunuka masu sauƙi zuwa matsakaici, in ji su.
Boeing da LATAM dai ba su amsa tambayoyi daga kamfanin dillancin labarai na Reuters ba game da musabbabin lamarin da kuma yanayin lamarin.
-Reuters
Dandalin Mu Tattauna