WASHINGTON, D. C. - Kasar da ke arewacin Afirka mai arzikin man fetur na daga cikin kasashen da ke aikin shigo da abinci da man fetur, tare da fatan biyan bukatun 'yan kasar Aljeriya da ke shirya liyafa na dare a lokacin da iyalansu ke bude baki lokacin azumin fitowar rana da zuwa faduwar rana.
Ga 'yan Algeria da ke tururuwa zuwa sabbin shagunan naman da aka shigo da su da mahauta sanye da fararen kaya, zuwan naman da aka shigo da shi daga nesa, daga nisan Ostiraliya ya tayar da hankalin murna da shakku.
“Bude shaguna irin wannan na faranta rai ga wadanda ba za su iya siyan naman kasar ba. Kamar yadda kuka gani, samfurin yana da inganci, kuma yana da kyau sosai, ” in ji wani malami mai ritaya Rabah Belahouane bayan jira a layi a wani sabon kantin na tsawon mintuna 30.
Algeriya ta dauki matakin na shigo da kayayyakin abinci ne da fatan kaucewa tashin farashin da ya shafi wadanda ba za su iya samun naman da ake samu a cikin kasar ba. Irin wannan hauhawar farashin kayayyaki ya addabi kasar a baya-bayan nan a shekarar da ta gabata lokacin da albarkatun albasa ya kasa biyan bukatar jama’ar kasar.
Makwabciyarta Tunisia na shirin shigo da ayaba daga Masar yayin da Mali ita kuma ke shirin karbar tallafin man fetur daga Rasha.
Ga Aljeriya, matakin shigar da nama ton 100,000 a wannan watan na Ramadan ya canja wata manufar hana shigo da kayayyakin a baya. An tsara wannan manufar don taimaka wa masu sana'a a cikin gida amma ta haifar da koma baya yayin da farashin naman a kasar ya tashi.
"Shawarar shugaban kasar ce ta sake bude hanyar kayayyakin da ake shigowa da su kasar domin baiwa talakawa damar cin nama a kan farashi mai sauki kuma ba za su hakura da mahauta da ke sayar da naman da tsada, ko da yake yana da inganci, kan farashin da ba zai yiwu ba," in ji Ministan Kasuwancin Aljeriya Tayeb Zitouni a makon jiya.
Shirin shigo da kaya ya zo ne yayin da farashin nama ke ci gaba da yin tsada dangane da matsakaicin kudin shiga da mafi karancin albashi a Aljeriya, da ke fama da matsalar hauhawar farashin kayayyaki da tsadar rayuwa.
-AP
Dandalin Mu Tattauna