Najeriya za ta ba da sabbin lasisin hakar ma'adinai ne kawai ga kamfanonin da suka gabatar da wani shiri kan yadda za a sarrafa ma'adanai a cikin gida, karkashin sabbin ka'idoji da ake samar da su, kamar yadda kakakin gwamnati ya tabbatar a ranar Alhamis.
Wasu jerin hare-hare da jiragen yakin Isra'ila suka kai kudancin Lebanon sun kashe mutane 16, yayin da wasu rokoki da kungiyar Hezbollah ta harba ta yi sanadiyyar mutuwar wani Ba'isra'ile daya, wanda ya zamar da ranar Laraba nan mafi muni cikin sama da watanni biyar na gwabza fada a kan iyakar kasar
Gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya bayyana amincewar gwamnatinsa na rage wa maniyyatan hajjin bana naira dubu 500 bayan da Hukumar Alhazan Najeriya ta kara naira miliyan 1.9 akan kudin hajjin bana.
Ana ci gaba da ƙoƙarin ayyukan ceto akan gadar Baltimore da ta rugurguje, inda masu aikin ceto a karkashin teku suka koma wurin da sanyin safiyar yau Laraba bayan rashin nasara saboda hazo cikin dare
Shugaban kasar Amurka, Joe Biden ya ayyana rugujewar gadar Baltimore a matsayin mumunar hatsari inda ya yi alkawarin sake gina babbar tashar jiragen ruwa dake gabashin kasar nan take bayan wata jirgin ruwa ta ci karo da gada
Dangantaka tsakanin Shugaba Joe Biden da Fira Ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ta fara yin tsami ne a Litinin bayan da Amurka ta amince da kudirin tsagaita wuta a Gaza a taron Majalisar Dinkin Duniya tare da kakkausar suka daga Shugaban na Isra'ila.
Akalla sojoji bakwai ne suka rasa rayyukansu yayin da wani bam ya tashi a Chadi a yayin da suke sintiri a yammacin kasar kusa da tafkin Chadi, in ji gwamnatin kasar.
Mawallafin Desert Heral da ke Kaduna, Tukur Mohammed Mamu, ya yi barazanar maka babban lauyan gwamnatin tarayyar Najeriya kuma ministan shari’a, Lateef Fagbemi (SAN), a kotu saboda ayyana shi a jerin masu daukan nauyin ta’addanci a kasar.
Dalibai shida na makarantar Kuriga da aka kubutar daga hannun masu garkuwa da mutane suna jinya a Kaduna, kamar yadda rundunar sojin ta bayyana a jiya.
Wani jirgin ruwan mai dakon kwantena ya kutsa cikin wata babbar gada da ke Baltimore a jihar Maryland da sanyin safiyar Talata, lamarin da ya yi sanadin karyewarta a wasu wurare tare da nutsewa cikin kogi.
Isra'ila ta fadawa wasu kasashen Turai hudu a yau Litinin cewa shirinsu na yin aiki don amincewa da kafa kasar Falasdinu ya zama "daukaka wa ta'addanci" wanda zai rage damar yin shawarwari na kawo karshen rikicin da ke tsakanin makwabtan.
Kungiyar agaji ta Red Crescent ta ce dakarun Isra'ila sun yi wa wasu asibitoci biyu kawanya a ranar Lahadin da ta gabata, inda suka yi ta luguden wuta kan jami'an kiwon lafiya, daga bisani Isra'ila ta ce ta kama 'yan ta'adda 480 yayin da aka ci gaba da gumurzu a babban asibitin Al Shifa na Gaza
Ofishin mai ba da shawara kan harkokin tsaro (ONSA) ya tabbatar da tserewar manajan yankin Binance na Afirka, Nadeem Anjarwalla daga Najeriya.
Domin Kari