WASHINGTON, D. C. - Hukumar kula da ‘yan cirani ta duniya IOM ta ce akalla wasu mutane shida kuma sun bace, ana kuma kyautata zaton sun mutu, yayin da Hukumar IOM da hukumomin yankin ke taimakawa wasu 22 da suka tsira.
Yvonne Ndege, mai magana da yawun hukumar IOM na yankin, ta ce hatsarin jirgin ya auku ne kimanin mita 200 daga kasar Djibouti kuma kwale-kwalen da ke dauke da bakin hauren ya taso ne da misalin karfe 2 na safe agogon kasar Yemen a ranar 8 ga watan Afrilu.
Kimanin sa'o'i biyu ne bayan tasowar jirgin ya nutse tare da mutane kusan 66, galibinsu 'yan yankin kuryar Afirka. An yi imanin yawancinsu 'yan kasar Habasha ne, in ji ta.
Ndege ta ce "Kowace shekara dubun-dubatar 'yan cirani ne ke barin yankin kuryar Afirka, musamman daga Habasha da Somaliya suke kokarin isa kasashen yankin Gulf."
"Amma dubban mutanen sukan makale a Yemen. Za a iya cewa gungun 'yan ciranin da suka mutu a wannan bala'in na kokarin komawa Djibouti ne domin samun karin lokaci sai su sake gwadawa daga baya ko kuma su koma gida."
-Reuters
Dandalin Mu Tattauna