ABUJA, NIGERIA —
A shirin Lafiya na wannan makon mun yi magana ne a kan yoyon fitsari da ya zama daya daga cikin matsalolin kiwon lafiya da ke shafar mata musamman wadanda suka fuskanci matsala a lokacin haihuwa.
A kokarin da ake yi na ganin cewa an shawo kan wannan matsala Gidauniyar Bashir Fistula Foundation tare da hadin gwiwar Babban Asibitin Gwarimpa da sauran masu ruwa da tsaki a bangaren sun bullo da wani tsari na yiwa mata masu fama da wannan matsalar aikin gyara kyauta.
Saurari cikakken shirin da Hauwa Umar ta gabatar:
Dandalin Mu Tattauna