A yayin da wutar rikicin gabas ta tsakiya ke matsawa zuwa Lebanon daga Zirin Gaza, fararen hula na arcewa zuwa kasashen makwabta. tun daga ranar 23 ga watan Satumbar da ya gabata, fiye da mutane dubu 425 sun ketara zuwa Syria daga Lebanon, a cewar Majalisar Dinkin Duniya.