Ana Shirin Kammala Yakin Neman Zaben ‘Yan majalisa a Gambia
Mutane da dama ne suka yi tattaki zuwa Majalisar Dattawan Najeriya domin gabatar da korafinsu na cewa a mayar da Sanata Ali Ndume wanda majalisar ta dakatar a makon da ya gabata, bayan da majalisar ta zarge shi da cewa ya kunyata ta a idon duniya bisa wani jawabi da ya yi a gabanta.
Nijar: Wasu kungiyoyin fararen hula sun shigar da kara suka bukaci a gudanar da bincike dangane da cinikin ma’adinin uranium.
Akalla mutane 10 ne suka mutu sama da wasu 50 kuma suka jikkata bayan wasu hare-hare a tashar jiragen kasa da ke tsakiyar birnin St. Petersburg.
Majalisar Dinkin Duniya ta baiwa Manjo Aichatou Issaka Ousmane, wata Soja daga jamhuriyar Nijar, lambar yabo akan irin rawar da ta taka a aikin Soja masamman a lokacin da aka tura ta yi aikin wanzar ta zaman lafiya a kasar Mali.
Nigeria: Barkewar cutar sankarau ta hallaka rayukan mutane kusan 300 yayin da kasar ke fuskantar karancin allurar rigakafi.
South Korea: An kama tsohuwar shugaba Park Geun-hye dangane da zargin cin hanci da rashawa da mulkin kama karya amma har yanzu hukumomi basu tuhume gaban kotu ba.
Ghana: Sabuwar gwamnatin Ghana na kokarin magance matsalar wutar lantarki a kasar ta hanyar yiwa dukkan ma’aikatunta na makamashi gyaran fuska.
Belgium: A hukumance, shugaban Tarayyar Turai, Donald Tusk ya amshi takardar gwamnatin Biritaniya, abinda zai share fagen ficewar kasar daga tarayyar turai.
Tsohon dan gwagwarmayar yaki da wariyar launin fata a Afirka ta kudu Ahmed Kathrada rasu yana dan shekaru 87 a Duniya
Egypt: Wata kotu ta yankewa mutane 56 hukuncin dauri na tsawon shekaru 7 zuwa 10 a dalilin samun su da hannu a mutuwar 'yan gudun hijira akalla 202 a cikin teku.
Domin Kari