Furucin Kakakin jam’iyyar ta ANC Zizi Kodwa, ya biyo bayan wani labari ne da jaridar karshen mako ta British Sunday Times ta buga, na cewa, Ma’akatar Leken Asirin ta CIA dake Amurka ta taimakawa gwamnatin wariyar wajen kama Nelson Mandela a 1962.
Rahoton da ya gutsuro maganar wani marigayin mai ritaya a ma’aikatar ta CIA da yace, Amurka ta kalli Marigayi Mandela a matsayin wani mai goyon bayan ‘yan ra’ayin gurguzu.
Mandela sai da ya shafe shekaru 27 a gidan yari, kama daga gwamnatin wariyar launin fata zuwa kan ta wadanda yake adawa da su a siyasance. An kuma zabe shi a matsayin shugaban kasa bakin fata na farko a shekarar 1994.
Kodwa ya fadawa kafofin yada labaran cikin kasar, cewa har yanzu ma’aikatan leken asiri CIA suna like da su suna kuma taimakawa masu son canjin gwamnati a kasar. Muryar Amurka ta so jin ta bakin Mista Zizi, amma ya ki daukar wayoyin da aka yi.