Tsoffin ministocin kasar Faransa mata su bakwai da suka hada da shugabar asusun bada lamuni ta IMF Christine Lagarde sun lashi takobin tunkarar cin zarafin da ake yiwa mata a harkokin siyasar kasar ta Faransa.
Jiya Lahadi a cikin mujallar da ake bugawa mako mako a kasar, wato Jornal Du Dimanche, matan suka lashi takobin wallafa duk furucin cin zarafi da musgunawa mata da ake yi da kuma irin halayyar da maza 'yan siyasa ke nuna musu.
Barazanar daukan wannan matakin ya biyo bayan wasu mata guda tara da suka koka tare da zargin cewa mukaddashin kakakin Majalisar Wakilan Faransa ya ci zarafinsu.
Tuni dai mukaddashin kakakin Dennis Baupin ya yi murabus saboda lamarin kodayake ya musanta zargin da matan tara suka yi tare da yin alkawarin kalubalantar zargin.