Wakilan majalisar sai da suka kutsa cikin mutane kafin su shiga zauren majalisar saboda masu zanga-zangar kin jinin Donald Trump da suka yi dafifi a harabarta inda Trump yake ciki ganawa da kakakinta, Paul Ryan.
Baicin nan yamutsin ya taso jiya Alhamis a hedkwatar Republican saboda wani sojan gona da ya yi shigar Donald Trump ya nuna irin rashin tabbas da akwai akan zabe mai zuwa. Wannan ko ya samo asali ne daga irin kalamun da Trump ya dinga yi wadanda yanzu sun raunata jam'iyyar a bainar jama'a.
Wani Dennis Rodriguez wanda ya jagoranci bakin haure da basu da takardun zama a Amurka sun yi kwaikwayon jana'izar jam'iyyar Republican. Sun ce ganawar da Trump ya yi da kakakin majalisar wakilai Paul Ryan bai canza komi ba. Jam'iyyar bata canza ra'ayinta ba akan wasu mahimman batutuwa wadanda a kansu ne Trump ya gina kemfen dinsa, lamarin da ya zama tamkar yiwa jam'iyyar tsirare ne gaban jama'a
Rodrguez yace "tun fil azar jam'iyyar Republican haka take. Babu banbanci tskaninta da ra'ayoyin Donald Trump. Furucinsa sun tona asirinsu ne. Sun nuna matsayinsu kuma yanzu kowa ya gane"
Cikin abubuwan da Trump ya dinga fada lokacin kemfen dinsa kafin ya samu kuri'un mutane miliyan goma sha daya yace zai tasa keyar mutane miliyan 11 da basu da takardar zama cikin kasar zuwa kasashensu na asali. Yace zai gina katanga tsakanin Amurka da kasar Mexico, kasar da ya zarga da turo barayi da masu fyade zuwa cikin Amurka. Zai kuma hana Musulmai shiga kasar.
Tuni dai 'yan jam'iyyar Democrats suka ce kin fitowa fili su goyi bayan Trump da jam'iyyar ke yi munafunci ne. Ra'ayinsu daya ne. Abun da Trump ke fada su ne suke cikinsu. Kalamun Trump sun bayyanawa jama'a jam'iyyar Republican a zahiri