John Kerry yana kokarin samun goyon bayan yarjejeniyar tsagaita wuta ne a Syria wadda yanzu take tanga tanga.
Sakataren harkokin wajen na Amurka ya gana da Sarki Salman wanda kasarsa ke goyon bayan 'yan tawayen dake kokarin hambarar da gwamnatin shugaba Bashar al-Assad, shugaban kasar ta Syria.
Kamfanin dillancin labarun Saudiya ya bada rahoton cewa John Kerry ya tattauna da sarkin akan yadda al'amura suke a kasar ta Syria da takwaransa na kasar Abdel Al Jubair.
Bayan ya kammala ziyarsa a Saudiya jiya Lahadin John Kerry ya tashi zuwa Vienna inda shi da takwaransa na kasar Italiya zasu jagoranci taron ministocin harkokin waje akan matakan tsaro da kuma samarwa gwamnatin Libya goyon baya.