A lokacin ziyarar, Kerry ya karawa kasar ta Albania kwarin gwiwa wajen karfafa matakan da ta ke dauka na samar da sauye-sauye a fannin shari’ar kasar.
Bayan wata ganawa da ya yi da Firai ministan kasar Edi Rama a yau Lahadi, Sakataren harkokin wajen Amurka ya ce ya gamsu da irin matakan da aka shata, wandada ake sa ran za su tallafawa bangaren shari’ar kasar.
A lokacin da ya ke jawabi, firai minister Rama, ya ce da ba dan Amurka ba, kasarsa ba za ta samu ci gaba a sauye-sauyen da ta ke yi ba.
Ita dai kasar ta Albania na shirin kwaikwayar tsarin shari’ar Amurke da na wasu kasashen nahiyar Turai, tare da samar da hukumar binciken manya laifuka, kwatankwacin FBI da ke Amurka.