Dan takarar neman shugabancin Amurka a jam’iyyar Democrat Bernie Sanders, da hamshakin mai kudin nan Donald Trump, sun lashe zaben fidda gwani da aka yi a jihar New Hampshire.
Wannan shi ne karon farko da ‘yan takarar biyu suka samu nasara a yunkurinsu na neman jam’iyyunsu su tsaida su a matsayin ‘yan takararsu.
Shi dai Sanders tuni ya samu kashi 60 na kuri’un ‘yan Democrat inda abokiyar hamayyarsa Hillary Clinton ta samu kashi 38.
Shima dai Trump ya samu kusancin hakan yayin da ya lashe kashi 35 wanda hakan ya bashi nasara cikin dandazon ‘yan takarar Republican.
A daya bangaren kuma, gwamnan Ohio John Kasich ya zo ne a matsayi na biyu a jam’iyyar ta Republican inda ya samu kashi 16
Wadannan sakamakon dai sun yi kusan daidai da zaben jin ra’ayin jama’a da aka yi, wadanda suka nuna cewa Sanata Sanders daga Vermont da Trump da ya fito daga New York za su samu nasara.