Masu bincike na tarraya a nan Amurka sun ce jirgin kasa na Amtrak da ya goce daga kan digarsa a jihar Washington. Wanda jami'an suka bayyana yana mahaukacin gudun mil 129 duk Sa'a 1 ne maimakon mil 48 cikin sa'a guda.
Jirgin ya goce ne daga kan digarsa a unguwar Dupont na jihar Washington da ke Arewa maso Yammacin Amurka a jiya Litinin, inda taragunsa har guda uku suka subuto daga kan wata gadar sama zuwa kasa kan babbar hanyar motoci har fasinjoji uku suka mutu da yawa kuma suka jikkata.
Wata Jami’a a hukumar kula lafiyar hanyoyin sufuri ta Amurka, Bella Dinh-Zarr, ta bayanawa manema labarai cewa, masu bincike suna bincikar na’urar jirgin kasan mai nadar bayanan yadda jirgin kasar ke tafiya, wacce suka ciro daga cikin taragon jirgin, wanda ya fara tafiyar farko akan sabuwar hanyar jirgin kasa mafi sauri.
Dinh-Zarr tace 'yan kwamitin tsaron sintiri na kasa zasu fara aikin su gadan-gadan a wajen da hatsarin ya auku daga yau Talata, kuma masu bincike zasu tattauna da maikatan jirgin domin gano inda aka yi kuskure da dalilin kuskeren da ya jawo hatsarin.
Facebook Forum