Kasar China tayi watsi da sukar lamirinta da Shugaba Donald Trump yayi a cikin sabuwar manufar tsaron kasarsa da ya gabatar, inda manufar ta ayyana China a zaman abokiyar adawa kuma kalubale ga akidojin Amurka.
Sabuwar manufar ta Trump ta soki lamirin shugabannin jam’iyyar Kwaminisanci ta China tare da zarginsu da kokarin yada tsarinsu na mulkin danniya a duniya da ma satar fasahar wasu mutane da kuma yada tsarin tattalin arzikinta da gwamnati ke kanainayewa.
Manufar ta bayyana wasu abubuwa guda uku da ke yin barazana ga zaman lafiya da kuma akidojin Amurka, baya ga kasashen Iran da Koriya ta Arewa da kuma kungiyoyin ta’addanci a duniya.
Manufar ta Amurka ta nuna China da Rasha a zaman manyan kasashen da ke kokarin shimfida wasu akidoji da muradu wadanda suka sha bamban da na Amurka a fadin duniya.
Facebook Forum