Jaridar New York Times ta ce an sayi zanen da sunan Yarima Bader bin Abdullah bin Mohammed bin Farhan al-Saud, amma an san shi babban aboki Yarima mai jiran gado, Mohammed bin Salman, ne, kuma an san ba ya da wata hanyar samun irin wannan kudi, sannan ba a san shi da tara zane-zane ba. Ba a taba sayen wani zane da tsada haka ba a tarihin duniya.
Zane Mai Suna "Salvator Mundi" ko "Macecin Duniya" Da Ake Zargin Yarima Mohammed bin Salman Da Saya A Kan Kimanin Naira Biliyan 160
- VOA Hausa

6
Fasta na Yarima Mohammed bin Salman mai jiran gadon sarautar Sa'udiyya a jikin allon da aka rubuta "Allah Ya kare ka" da larabci a kan wata hanya a kasar Lebanon.

7
'Yan wasa a lokacin wasu bukukuwa na Sa'udiyya karkashin wani makeken hoto na Yarima mai jiran gado, Mohammed bin Salman a filin wasa na Sarki Fahd dake Riyadh, ranar 23 Satumba 2017.