Hukumar lafiya ta duniya, tare da hadin guiwar asusun tallafawa kananan yara UNICEF, da kulob din Rotary da kuma asusun tallafi na Bill da Melinda Gates suna kokarin yiwa sama da kananan yara miliyan daya da dubu dari da goma sha daya allurar rigakafin shan inna a nahiyar Afrika cikin kwanaki hudu, da niyar shawo kan cutar da bata da magani da tuni aka shawo kanta a kasashen yammaci.
Za a fara aiwatar da shirin ne yau jumma’a a kasashe goma sha tara na nahiyar daga cikin ishirin da aka yi shirin gudanarwa tun farko, banda Najeriya sabili da cikas da aka gamu da shi a kasar, ya sa tilas a daga ranar da za a fara rigakafin zuwa ranar 31 ga watan Maris zuwa 3 ga watan Afrilu shekara ta 2012.
Shirin rigakafin da za a fara yau zai kunshi amfani da ma’aikatan sa kai da zasu shiga gida gida suna digawa kananan yara maganin rigakafin.
Wannan na daga cikin kamfen kasa da kasa na yaki da cutar shan inna da ta hada kan gwamnatoci da hukumar lafiya ta duniya da asusun UNICEF, da cibiyar yaki da cututuka ta Amurka (CDC) da kuma kungiyoyi masu zaman kansu.
A halin da ake ciki dai ma’aikatar lafiya ta kasa a Najeriya da cibiyar kiwon lafiya matakin farko, tare da hadin guiwar likitocin jinyar kananan yara da cibiyar rigakafi ta John Hopkins sun gudanar da wani taron koli kan allurar rigakafi a birnin tarayya Abuja da nufin shawo kan cuttukan da ake iya magancewa ta wajen allurar rigakafi.