Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ayyana dokar ta baci kan cutar Polio


Mutane suna karban maganin cutar Polio
Mutane suna karban maganin cutar Polio

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ayyana dokar ta baci kan yaki da cutar shan inna, yayinda za a yi jinyar sababbin kamun cutar da gaggawa.

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ayyana dokar ta baci kan yaki da cutar shan inna, yayinda za a yi jinyar sababbin kamun cutar da gaggawa.

Karamin ministan lafiya Dr. Mohammad Pate ne ya sanar da haka a wata sanarwa da ya bayar dauke da rattaba hannun mataimakinshi kan harkokin watsa labarai da hulda da jama’a Mr. Tashikalmah Hallah, a Abuja.

Ministan wanda yayi wannan furucin a wajen wani taron kwamitin shugaban kasa kan yaki da cutar shan inna ya kara da cewa, “gwamnati ta kuduri aniyar kawo karshen yaduwar kwayar cutar shan inna a Najeriya, zamu kuma dauki dukan matakai wajen ganin an yiwa ‘ya’yanmu rigakafi”.

Kwamitin yaki da cutar shan innan zai yi aiki tare da hadin guiwa da gwamnoni da shugabannin kanannan hukumomi da cibiyoyi ko kungiyoyin dake yaki da cutar, da sarakunan gargajiya da kuma shugabannin addinai da nufin ganin an shawo kan yada cutar kafin shekara ta 2015.

Dr. Pate ya bayyana cewa, kwamitin ya amince da yin aiki tukuru wajen ganin an shawo kan cutar a karshen shekara ta 2012 a maimakon 2015. Ya kuma bayyana cewa inda kwamitin zai maida hankali sun hada da jihohin da ba a sami bulla cutar ba na tsawon watanni shida domin ganin ba a sake samun cutar ba a shekara 2012 baki daya.

Ya kuma ce za a bukaci jihohin da suka sami fiye da yaro daya dake dauke da kwayar cutar a cikin watanni 12 da suka shige, su yiwa sama da kashi 90% rigakafi. Ministan ya kuma bayyana cewa za a kafa irin wannan kwamitin a jihohin da basu da shi.

Bisa ga cewar ministan lafiyan, tilas ne masu yin allurar rigakafi su tabbata cewa an yiwa kowanne yaro allurar rigakafi. Ya jadada cewa idan aka sami yaro daya da kwayar cutar, ana bukatar gudanar da cikakken bincike a kuma kai rahoto nan da nan.

Dr. Pate ya bayyana cewa, kasar Indiya ta sami nasarar shawo kan cutar ne sabili da gagarumin aikin rigakafi da kuma kyakkyawan sa ido kan cutar. Ya kuma shawarci jami’ an sa ido kan aikin rigakafin su isa jihohin da zasu yi aiki mako guda kafin ranar fara aikin rigakafin domin tabbatar da nasarar shirin.

Melinda Gates

BIDIYO: COVID-19 VOA Ta Yi Hira Da Melinda Gates Kan Dalilin Da Yasa Suke Taimakawa Afirka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG