Hukumar lafiya ta Duniya tace, zazzabin lassa ya kashe mutane dubu biyar a Yammacin Afurka, zazazabin da ya kuma yi sanadin mutuwar a kalla mutane 40 da dama kuma suna kwance a asibitai a kimanin kashi daya bisa uku na jihohi 36 a Najeriya a cikin makonni shida da suka shige.
Wani jami’in ma’aikatar rigakafin miyagun cututuka a Najeriya, Henry Akpan a Najeriya ya bayyana cewa, wadanda suka rasa rayukansu sun hada da likitoci biyu da ma’aikatan jinya nus-nus shida sakamakon barkewar zazzabin lassa a jihohin kasar 12.
Bisa ga cewarshi, an sami rahoton mutane 397 da suka kamu da cutar aka kuma tabbatar da 87 daga ciki.
Kwayar cutar lassa dai cuta ce da take shiga jini, an kuma fi samunta a kasashen dake Yammacin Afrika da suka hada da Saliyo da Liberia, da Guinea da kuma Senegal.
Ana kamuwa da cutar ne ta wajen taba kashin beran dake dauke da cutar.
Alamun cutar sun hada da zazzabi da ciwon kai, da hadiya da kyar, cutar tana kuma iya shafar muhimman gabobin jiki ta kai ga kisa. Sunan ya sami asali ne daga sunan wani kauye da ake kira Lassa a jihar Borno, inda aka fara tantance cutar a shekara ta dubu da dari tara da sittin da tara.