An sami bullar shan inna a jihar Naija karon farko cikin shekaru uku. Jihar Naija ta sami koma baya a yunkurinta na shawo kan ciwon shan inna a jihar sakamakon samun wani yaro dauke da cutar a Unguwar Birni, dake mazabar Bangi cikin Karamar Hukumar Mariga.
A jawabinshi ga manema labarai a Minna, babban birnin jihar Naija bayan tabbatar da bullar cutar, kwamishinan lafiya na jihar Dr. Ibrahim Sule yace, Fulani makiyaya iyayen wani yaro ne da ya nakasa sakamakon kamuwa da ciwon shan inna, da suka kaura daga jihar Zamfara suka dauke da kwayar cutar.
Bisa ga cewarshi, iyayen yaron sun kaura ne daga jihar Zamfara sakamakon rikicin al’umma, suka yada zango a unguwar Biri. Yace an sami bullar cutar ne sakamakon dauko kwayar cutar daga aka yi daga wata jiha zuwa wata.
Kwamishina ya bayyana cewa, an dauki matakin shawo kan lamarin ba tare da bata lokaci ba, bayan samun bullar cutar. Duk da yake mahaifin yaron ya bayyana cewa, an yiwa yaron allurar rigakafi a jihar Zamfara, kwamishinan ya bayyana cewa, nakasa yaro da cutar tayi ya nuna cewa, iyayen basu bada badin kai a shirin rigakafin ba.
Kwamishinan ya kuma bayyana cewa, gwamnatin jihar ta kafa wani kwamitin binicke da ya kunshi jami’an hukumar lafiya ta dubiya da asusun tallafawa kananan yara UNICEF da kuma shirin lafiya matakin farko.