Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana kara samun yara dauke da cutar shan inna a Najeriya


Ana digawa wani yaro maganin rigakafin shan inna
Ana digawa wani yaro maganin rigakafin shan inna

Ana ci gaba da samun kananan yara dauke da cutar shan inna a Najeriya duk da ikirarin da kasar ke yin a shawo kan yaduwar cutar

Ana ci gaba da samun kananan yara dauke da cutar shan inna a Najeriya duk da ikirarin da kasar ke yin a shawo kan yaduwar cutar kafin karshen shekara ta dubu biyu da goma sha biyu.

Rahotanni na baya bayan nan sun bayyana bullar cutar a jihar Kaduna inda aka shafe shekaru biyu ba tare da an sami ko yaro daya dauke da cutar ba.

Ta dalilin haka, gwamnatin jihar Borno ta kafa wani kwamiti mai karfi da nufin ganin nasarar shirin rigakafin da ake kyautata zaton zai kai ga shawo kan cutar a kasar baki daya.

Shugaban kwamitin, Baba Kaka Bashir Garbai ya bayyana cewa, gwamnatin jihar zata dauki matakai na ganin cew, ba a sake samun bullar cutar ba a jihar Borno. Ya kuma bayyana cewa, gwamnatin jihar ta kara kason kudin da take kashewa a kan yaki da cutar yayinda yace kwamitin zai bada karfi wajen amfani da sarakunan gargajiya tare da kara fadakar da jama’a dangane da amfani maganin.

Bisa ga cewarshi, kwamitin zai kuma bi ta kungiyoyin addinai domin kaiwa ga al’ummomin jihar baki daya. Yace burin kwamitin shine ganin babu yaro ko daya dake dauke da cutar a jihar da ta kasance daya daga cikin jihohin arewacin kasar da ake fuskantar barazanar yaduwar cutar kasancewa iyaye basu yarda a yiwa ‘ya’yansu rigakafin sabili da shakku da rashin yarda.

Melinda Gates

BIDIYO: COVID-19 VOA Ta Yi Hira Da Melinda Gates Kan Dalilin Da Yasa Suke Taimakawa Afirka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG