A ranar Litinin ma'aikatar shari’a ta umurci masu gabatar da kara na tarayya a New York da su yi watsi da tuhume tuhumen da akewa magajin garin New York Eric Adams, cewar wata takarda da ta fito daga mukaddashin babban mai shari’a Emil Bove.
Bove, wani wanda shugaba Donald Trum ya yiwa nadin siyasa, ya shiga Tsakani a karar, inda ya ce, kama Adams da laifi ya ci karo da yakin neman sake zaben shi a matsayin magajin gari a shekarar 2025.
Wani mai magana da yawun ofishin babban mai shari’a na Amurka a Manhattan, wanda ya shigar da tuhume tuhumen yaki cewa uffan akan batun.
Ya zuwa yanzu dai masu gabatar da karan ba su mika wani hanzari ba ga alkalin dake kula da shari’ar, wani alkalin yanki Dale Ho dake Manhattan, cewa suna da niyyar yin watsi da karar.
An dai yi karar Adam bisa tuhume tuhume har biyar, da ya hada da amsar alfarmar guzuri daga jami’an Turkiyya da gudummuwar siyasa daga 'yan wata kasa domin daukar wasu matakan amfanar da Turkiyya.
Adams bai amince da aikata wani laifi ba.
Dandalin Mu Tattauna