An gano wasu yara da shekarun su basu wuce na yara yan makaranta ba, a wani karamin gari a Arewacin Texas ta Amurka su 15 dauke da cutar kyanda, da ya kasance koma baya wajen samun rigakafi a jihar.
Shugaban sashen lafiya na yankin South Plains, Zach Holbrooks ya fada a ranar Litinin cewa, an sanar da hukumar shi labarin bullar cutar kan yara biyu a yankin Gaines a karshen watan Janairu, yaran kuma sun ga likita a Lubbock.
Holbrooks, ya ja hankali kan cewa, ana cigaba da gudanar da bincike a kan lamarin, da cewa, wasu daga cikin yaran da suka kamu da cutar, bisa ga dukkan alamu suna da nasaba da wata makarantar addini mai zaman kanta dake yankin.
Ya kara da cewa, ‘bazan iya cewa duk suna da nasaba da hakan ba, to amma ayarin mu na duba wuraren da suka yi alaka da su, da inda cutar ta samo asali.’’
Jami’an lafiya a yankin sun samar da wani wurin karbar rigakafi na tafi da gidan ka a makon jiya, suna kuma kula ta aikin gwaji ga mazauna yankin.
A shekarar 2024 ne dai Amurka ta ci karo da karuwar masu dauke da cutar ta kyanda, da ya hada da barkewar ta a Chicago, inda mutane sama da 60 suka kamu. A wannan watan jami’an lafiya a metro Atlanta na aiki domin shawo kan cutar ta kyanda da ta watsu zuwa tsakanin wasu iyalai biyu da ba su yi rigakafi ba.
Dokar Texas ta ba yara damar tsame kansu daga karbar rigakafi a makaranta, bisa dalilan rashin aminci a zuci da ya hada da batun addini. Yawan yaran dake da irin wannan dama ya karu a cikin shekaru goman da suka wuce da kashi 76 daga cikin 100 a shekarar 2014 a cewar alkaluman hukumar lafiya ta jihar Texas
Dandalin Mu Tattauna