A yau Litinin Amurka da Cuba suka maido da cikakkiyar huldar dipolomasiyya ta hanyar bude ofisoshin jakadancinsu da misalin karfe goma 12 na safiyar yau Litinin, bayan da suka kwashe sama da shekaru hamsin suna zaman doya da manja.
Da sanyin safiyar yau ne aka daga tutar kasar Cuba mai launin ja da shudi a ma’aikatar cikin gidan Amurka tare da sauran na kasashe dake huldar diplomasiyya da Amurka.
Hakan na nufin kasashen biyu sun maido cikakkiyra hulda ke nan a tsakaninsu
Hakan kuma na zuwa ne bayan shekaru 54 da kasashen suka kwashe suna gaba da juna tun daga zamanin shugabancin tsohon shugaban Amurka John Kennedy.
A yau Litinin ake sa ran jam’ian Cuba ciki har da Ministan harkokin wajen Cuba, Burno Rodriguez Parilla za su halarci wani biki a ofishin Jakadancin Cuba da ke nan Washington