Shugaban kasar Cuba Raul Castro ya kai ziyara fadar Vatican jiya Lahadi, domin godewa Paparoma Francis da kashin kansa, sabili da rawar da ya taka wajen kawo karshen kallon hadarin kaka na tsawon shekaru hamsin tsakanin Amurka da Cuba, abinda da ya sa kasashen suna kokarin sake kulla huldar diplomasiya.
Shugaban kasar Cuban ya gana da Paparoma Francis haifaffen Agentina na tsawon kusan sa’a guda, inda suka tattauna da harshensu na Spaniyanci.
Paparoma Francis, shugaban darikar Katolika na duniya, shine ya taka muhimmiyar rawa a tattaunawar sirrin da aka yi tsakanin Cuba da Amurka da ta kai ga sanarwar da aka yi a watan Disamban bara cewa, kasashen biyu suna daukar matakin sake bude ofisoshin jakadancinsu a manyan biranen kasashensu, da kuma fadada huldar cinikayya. Fadar Vatican tace Paparoma Francis wanda shine Paparoma na farko daga kudancin Amurka, da kansa ya shiga tsakanin kasashen biyu ya kuma karbi bakuncin wakilan kasashen biyu yayin tattaunawar.
A lokacin da yake barin fadar Vatican, Mr Castro yace, “na godewa Paparoma sabili da abinda yayi”. Daga baya ya kuma yabawa irin basira da kamilci da kuma halayen kwarai na Paparoman.
Fadar Vartican ta ba Mr. Castro lambar girmamawa ta St Martin of Tours, ta fice a fannin kula da gajiyayyu. Mr. Castro ya bayyana niyarsa ta halartar duka taron sujada da Paparoma zai jagoranta idan ya kai ziyara kasar Cuba a watan Satumba, kafin ziyarar da zai kai Amurka da kuma ganawa da shugaba Barack Obama.