Jiya Jumma’a a Havana,shugaban juyin juya hali a Cuba Fidel Castro, ya gargadi ma’aikatan difilomasiyyar kasar su yi hattara, domin akwai yi yuwar a gwabza yaki da makaman Nukiliya. Castro wanda ya ziyarci Ma’aikatar harkokin wajen Cuba a Havana, ya yi hasashen za’a gwabza yakin da makaman kare dangin, idan Amurka da Isra’ila suka ci gaba da matsin lamba a kakabawa Iran takunkumi kan shirin Nukiliyarta.
Haka kuma ya yi hasashen Amurka za ta kai wa KTA hari.
Tsohon shugaban kasan ya amsa tambayoyi fiyeda sa’a daya da rabi daga jakadu.
Tun watan Yuli a 2006 ne aka daina ganin Castro a bainar jama’a,bayan an yi masa tiyata a hanji,sakamakon haka ya mika iko ga kanin sa Raul Castro, wadda ahalin yanzu shine shugaban kasa.