Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wata mace zata yi iyo daga kasar Cuba zuwa Amirka

Diana Nyad, a lokacinda ta fara kokarin yin iyo daga kasar Cuba zuwa nan Amirka a ranar juma'a.
Diana Nyad, a lokacinda ta fara kokarin yin iyo daga kasar Cuba zuwa nan Amirka a ranar juma'a.

A ranar juma’a da maraice, wata mace mai suna Diana Nyad yar shekara sittin da biyu da haihuwa ta fara iyo daga gabar tekun birnin Havana kasar Cuba zuwa jihar Florida. Ana sa ran Diana zata yi iyon kilomita dari da sittin da shidda cikin sa’o’i sittin, kafin ta kamalla.

Wasu mutane cikin ayarinta ne cikin kwale kwale suka raka ta, wadanda suke bata abinci da magani da sauran abubuwan da take bukata.

Watani biyu da suka shige tayi wannan yunkuri amma bata samu nasara ba, kuma ta dage akan cewa ba yawan shekarunta ne suka hana ta samun nasara ba, amma ciwon asma ne ya tilasta mata ta janye.

Ita wannan mace Diana ta taba wannan yunkuri na yin iyo daga Cuba zuwa jihar Florida tana da shekaru ashirin da takwas da haihuwa, amma dole ta dakata domin iska mai karfi da igiyar ruwa.

Idan tayi nasara, to zata zama mace farko data yi wannan yunkuri ba tare da kariyar caji daga harin kifin teku ba.

XS
SM
MD
LG