Shugaba Barack Obama na Amirka ya kare matakin daya dauka na kokarin sake maida huldar jakadanci tsakanin Amirka da kasar Cuba, yana mai fadin cewa daukan wannan mataki zai baiwa Amirka damar shawo kan kasar mai bin akidar kwaminisanci.
Shugaba Obama yayi wannan furuci ne wajen wani taron yan jarida na karshen shekara a fadarsa ta White House a jiya Juma'a.
Yace baya sa ran cewa cikin dare aga wani canji a kasar Cuba, kuma kila a dauki lokaci kafin Majalisar dokoki Amirka ta fara yin muhawara akan yiwuwar dage takunkumin cinnikaya da tsibirin na Cuba. To amma duk da haka shugaba Obama yace, a fili ne cewa maida kasar Cuba saniyar ware bai sa kwaliya ta biya kudin sabulu ba.
Yace shi yana ganin cewa idan aka yi shekaru hamsin ana daukar wasu matakai, amma kuma baga canji ba, to ya kamata a dauki wasu matakan kuma idan har ana son biyan bukata ko kuma samun nasara.
Shugaba Barack Obama na Amirka ya kare matakin sake maida huldar jakadanci tsakanin Amirka da Cuba.