A yau Talata, hukumar lafiya ta duniya (WHO) ke kaddamar da wani sabon dandali da rika samarda maganin cutar sankara kyauta ga dubban kananan yaran dake zaune a matalautan kasashe, a wani yunkuri na inganta damar su ta rayuwa dake matukar raguwa.
Za'a mika rukunin farko na magungunan zuwa ga kasashen Mangoliya da Uzbekistan, a cewar WHO, inda aka tsara aika karin magungunan ga kasashen Ecuador da Jordan da Nepal da kuma Zambia a wani bangare na gabar gwaji ta aikin.
Ana sa ran magungunan su kai ga kimanin yara 5,000 masu fama da larurar sankara a bana a akalla asibitoci 30 dake kasashen 6.
Ana sa ran kasashen El-Salvador da Maldova da Senegal da Ghana da Pakistan da kuma sri lanka su bi sahu nan bada jimawa ba.
Dandalin na fatan kaiwa ga kasashe 50 nan da shekaru 5 zuwa 7, yana samar da magunguna ga akalla yara 120, 000.
Dandalin Mu Tattauna