Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Cika Shekaru Hudu Cif Da Sace ‘Yan Matan Chibok


Cikar 'Yan Matan Chibok Shekaru Hudu a Hannun Boko Haram
Cikar 'Yan Matan Chibok Shekaru Hudu a Hannun Boko Haram

A yau ranar 14 ga Afrilu ne ‘yan matan da aka sace a garin Chibok na Jihar Borno, suka cika shekara hudu ba tare da ansan inda suke ba ko halin da suke ciki.

Ranar 14 ga watan Afrilun shekarar 2014 ne wasu mayakan kungiyar Boko Haram suka sace dalibai ‘yan mata 276, a makarantarsu da ke garin Chibok a jihar Borno.

‘Yan mata 57 sun gudo da kansu, sannan a watan Oktoba na shekarar 2016 gwamnatin Najeriya ta karbo ‘yan mata 21, sannan sojoji suka uku, wanda jimilla ta zama 81.

Duka dai ‘yan mata 107 ne gwamnati ta iya karbowa a cikin shekaru hudu.

Yanzu haka dai akwai sauran ‘yan mata 112 a hannun kungiyar Boko Haram.

Cikin shekara hudun ne aka samu wata kungiya da ake kira ‘Bring Back Our Girls’ da ke fafutukar ganin an kwato ‘yan matan, wanda yunkurin da kungiyar ta yi ne ya sa aka san labarin sace ‘yan matan a duk fadin duniya.

Cikar 'Yan Matan Chibok Shekaru Hudu a Hannun Boko Haram
Cikar 'Yan Matan Chibok Shekaru Hudu a Hannun Boko Haram

Kungiyar kullum tana yin zama a dandalin hadin kan kasa na Unity Fountain da ke Abuja.

Ana kuma cikin wannan hali ne aka sami labarin sake sace wasu dalibai na makarantar sakandare ta Dapchi da ke jihar Yobe, a halin yanzu an dawo da 104 saura yarinya guda mai suna Leah Sharibu.

Domin karin bayani saurari cikakken rahotan Medina Dauda.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:23 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG