Rahoton da Amnesty International ta fitar ya nuna Najeriya ce kan gaba a nahiyar Afirka wajen zartas da hukumcin kisa.
Kungiyar ta yabawa sauran kasashen Afirka, musamman kasar Guinea wadda ta kasance ta ishirin wajen kawo karshen yanke hukumcin kisa.
Kasar Kenya ta bi sawun kawar da hukumcin kisa a kasarta. Kasashen Burkina Faso da Chadi na daukan matakan da zasu kai ga daina yanke hukumcin kisa a kasashensu.
Alhaji Musa Jika daya daga cikin ‘ya’yan kungiyar Amnesty International a Najeriya yace rahoton ya nuna cewa ya kamata alkalan kasashe irinsu Najeriya da gwamnati su dinga kula da yanayin shari’a a kasarsu. Yace barazanar hukumcin kisa ba zai magance wasu matsaloli ba, gara ma a ce an yake wa mutum hukumcin daurin rai da rai.
Rahoton dai ya yi kira ga gwamnatin Najeriya da ta kawo karshen hukumcin kisa a kasar. Matakin yin hakan ya dogara ne ga majalisun dokokin kasar. Alhaji Musa Jika y ace wajibi ne da yake rataye akan ‘yan majalisa su yi dokar kawar da hukumcin kisa.
Ga rahoton Babangida Jibrin da karin bayani
Facebook Forum