Jami’in hukumar dake yaki da fataucin mutane Mr. Josiah Emeron ya yiwa Muryar Amurka karin bayani akan ceto wasu.
‘Yan mata 19 dukansu ‘yan asalin jihar Kano da ake kokarin safararsu zuwa Saudiya.
Inji Mr Emeron nasarar tasu ta biyo bayan wani bayanan sirri da suka samu ne akan yara kananan a lokacin da ake dab da jigilarsu su zuwa kasar Saudiya. Yace ana tura yaran ne da suna zasu je su yi aiki ne amma daga bisani kuma sai a mayar dasu bayi, su dinga aikin bauta.
Shugabar kare hakkin mata a Najeriya Dr. Saudatu Mahadi tace irin wannan balaguron nada manyan illoli guda uku. Illa ta daya itace muddin suka tsallake daga kasarsu sun shiga inda basu da daraja ke nan. Ta biyu itace wulakanci da ake nuna masu. Illa ta uku ita ce budewa ‘ya’ya mata wata hanyar kwadayi da zai sa su shiga yin wasu muggan halaye.
Masanin halayyar bil Adama Farfesa Muhammad Tukur Baba ya baiyana dalilin da ya sa ake irin wannan tafiyar. Ya ce kowa yana tsammanin idan ya bar inda yake zuwa wani wurin zai samu jin dadi.
Shugaban hukumar wayar da kawunan ‘yan Najeriya Dr. Garba Abari ya ce dole ne gwamnatocin tarayya da na jihohi da shugabannin addini su tashi tsaye su dakile matsalar. Yace, su a hukumance suna fadakar da jama’a akan illar safarar mutane tare da yin maganin talauci wanda ke sa mutane barin kasarsu .
Ga rahoton Hassan Maina Kaina da karin bayani
Facebook Forum