Ana ci gaba da yin cece-kuce akan anniyar Shugaba Buhari na sake tsayawa takara a zaben shugaban kasa na shekarar 2019.
Tijjani Yahaya Kaura wani dan majalisa ya bayyana ra’ayinsa akan sake tsayawar Shugaba Buhari takara. Cikin shekaru biyu da watanni tara da shugaban ya yi yana mulki ya taka rawar gani a cikin gida Najeriya da ma kasashen waje inji Yahaya Kaura.
Sanata Umar Ibrahim Kurfi y ace sun godewa Allah shugaban ya yadda ya sake tsayawa domin a cewarsa basu da wani da ya fi shugaban saboda a duk fannin da aka dubi shugaban babu wanda ya kai shi.
A bangaren Majalisar Wakilai mataimakiyar shugaban marasa rinjaye a majalisar Binta Bello ita ma ta yi tsokaci akan wannan batu. Tace su ‘yan adawa basu da matsala da fitowar shugaban domin hukumci yana hannun ‘yan kasa da zasu jefa kuri’u.
Shi ma dan majalisar wakilai Muhammad Umar Bago ya yi karin haske akan lamarin tare da bada hujjojin goyon bayan shugaban.
Ga rahoton Medina Dauda da karin bayani
Facebook Forum