Shelkwatar tsaron Najeriya ta kaddamar da aikin wanzar da zaman lafiya mai taken “Operation Safe Corridor” a shiyar arewa maso yammacin kasar a hukumance, inda aka kafa cibiyar a karamar hukumar Tsafe, ta jihar Zamfara.
Manufar shirin ita ce dakile matsalar rashin tsaro ta hanyar samar da tsarin sake tsugunarwa tare da shigar tubabun ‘yan ta’addar da suka mikamakamai bisa raddin kansu cikin al’umma.
Yayin bikin mika ginin da zai zamo shelkwatar aikin wanzar da zaman lafiyar a hukumance, Gwamna Lawal Dauda ya jaddada aniyar gwamnatinsa ta tallafawa hukumomin tsaro wajen yaki da laifuffuka.
An tsara aikin wanzar da zaman lafiyar “Operation Safe Corridor” ne domin baiwa tsaffin masu tada kayar baya da ‘yan bindiga damar komawa cikin al’umma.
Dandalin Mu Tattauna