Fashewar da garin harsashin bindiga ya haddasa a kasuwar Talatar-Mafara dake jihar Zamfara, ta hallaka mutane 2.
Al’amarin daya faru a jiya Talata, ya haddasa tsananin fargaba inda ‘yan kasuwa da masu sayen kaya suka rika gudun neman tsira a kasuwar mai yawan hada-hada.
Wani ganau yace fashewar ta samo asali ne daga wani kanti da ake sayar da bindigogi kirar gida.
Shugaban karamar hukumar Talatar Mafara, Yahaya Yari, ya tabbatar da afkuwar lamarin a yau Laraba.
Ya kuma bayyana cewar an garzaya da mutanen da suka jikkata sakamakon fashewar zuwa asibitin koyarwa na jami’ar Usman Danfodio dake Sokoto domin samun kulawa.
Dandalin Mu Tattauna