Hukumomi a Nigeria sun ce wani bam din da ya tarwatse a birnin Kaduna da ke arewacin Nijeriya, ya hallaka mutane da dama.
Wani ganau ya ce bam din ya tashi ne a wani wurin hada-hada da ke kusa da wata Majami’a a daidai lokacin da jama’a da dama ke harmar zuwa ibadar Easter. Nan da nan dai babu wanda ya dau alhakin kai harin.
Fashewar ta biyo bayan wani gargadin da wasu jami’an diflomasiyyar kasashen waje su ka yi cewa akwai yiwuwar kai hari a wasu muhimman ranakun Kirista na wannan shekarar.
Nijeriya ta dandana wasu tashe-tashen bama-baman kuma sau 4 ran Kirsimetin da ya gabata da su ka hallaka mutane akalla 44, ciki har da wasu da dama da aka kashe a wata Majami’ar Katolika da ke kusa da Abuja, babban birnin kasar.
Tsattsaurar kungiyar Islamar nan ta Boko Haram, ta dau alhalin abin da ya yi kama da tsararren hare-hare.