Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta kara yawan kason kudin yaki da cutar Polio


Ana ba yaro maganin cutar Polio
Ana ba yaro maganin cutar Polio

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta kara kason kudin yaki da cutar shan inna daga dala miliyan 17 zuwa dala miliyan 30

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta kara kason kudin yaki da cutar shan inna daga dala miliyan 17 zuwa dala miliyan 30 tare da alkawarin kara kudin idan akwai bukatar yin haka.

Gwamnatin tarayya ta kuma bayyana cewa, yawan al’umma a kasar bai zama hujjar gaza shawo kan cutar ba kasancewa kasashen dake da biliyoyin al’umma sun iya shawo kan cutar.

Shugaba Goodluck Jonathan ne ya sanar da haka yayin kaddamar da kwamitin shugaban kasa na musamman kan yaki da cutar shan inna. Ya bayyana cewa abin kunya ne ganin har yanzu ana samun kwayar cutar shan inna a Najeriya duk da yake cutar tafi kowacce saukin magancewa ta wajen rigakafi.

An umarci kwamitin ya rika ba shugaban kasa rahoton ci gaban da aka samu kai tsaye kowanne wata, da kalubala da ake fusakanta da kuma matakan gyara da aka dauka na shawo kan cutar shan inna a Najeriya.

Kwamitin dake karkashin jagorancin karamin ministan lafiya Dr. Alli Pete zai maida hankali ne kan kananan hukumomi da jihohin da cutar tafi barazana da sa ido kan ci gaban da suke samu kowanne wata.

Shugaba Jonathan wanda ya bada tabbacin cewa, ba zai janye alkawarin da yayi a wajen taron CHOGM da aka yi a Australia ba, na raba kasar da cutar shan inna kafin ya bar mulki a shekara ta 2015, ya yabawa gwamnoni domin mika wuyansu da cewa, daga cikin jihohin kasar 36, da babban birnin tarayya Abuja, yanzu an sami cutar a jihohi takwas ne kadai da suka hada da Kano, Jigawa, Katsina, Sokoto, Zamfara, Kebbi, Borno da kuma Yobe.

Shugaba Goodluck Jonathan ya kuma godewa kungiyoyi da cibiyoyi da kuma kasashen da suka hada hannu da Najeriya a yunkurin yaki da cutar shan inna da suka hada da gwamnatocin Japan, da Birtaniya, da Amurka da Jamus da kulob din Rotary da kuma gidauniyar Bill da Milinda Gates.

Melinda Gates

BIDIYO: COVID-19 VOA Ta Yi Hira Da Melinda Gates Kan Dalilin Da Yasa Suke Taimakawa Afirka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG