Amurka ta gargadi ‘yan kasarta da ke Nijeriya cewa da alamar tsattsaurar kungiyar Islamar nan ta Boko Haram na shirin kai hare-hare a babban birnin tarayyar Nijeria, Abuja.
Ofishin jakadancin Amurka ta aike da sakon gaggawa cewa mai yiwuwa a hare-haren a auna otal-otal din da ‘yan kasashen Yamma kan sauka, to amman ba a san lokacin ba.
Gargadin ya ce gwamnatin Nijeriya na sane da barazanar kuma ta na daukar matakan tsaro sosai.
Ofishin Jakadancin Amurkar ya shawarci Amurkawa da su kula sosai da tsaron lafiyarsu a cibiyoyin gwamnatin Nijeriya, da gine-ginen jakadanci, da wuraren da jama’a kan yi cincirindo, da kasuwanni da kuma wuraren ibada.
Ofishin ya aike da gargadi makamacin wannan a cikin watan Oktoba bayan wasu jerin munanan hare-haren da aka kai a arewacin Nijeriya. To amman gwamnatin Nijeriya ta soki lamirin gargadin. Ta ce hanzarin Amurka din bai biyo bayan samin wani sabon bayani ba, kuma hakan yawaita tayar da hankali ne kawai na babu gaira babu dalili.
Ana zargin Boko Haram da kai wani harin bam a farkon wannan watan da ya hallaka mutane da dama, to amman ba ta dau alhakin kai harin ba.