Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutane shida sun mutu a wasu fashe-fashe a Nijeriya


'Yan sanda da 'yan agaji a harabar jaridar This Day da aka kai wa hari a Abuja
'Yan sanda da 'yan agaji a harabar jaridar This Day da aka kai wa hari a Abuja

Hukumomi sun ce wani harin bam din da aka kai a wani gidan jarida a babban birnin tarayyar Nijeriya, Abuja ya hallaka mutane 3

Hukumomi sun ce wani harin bam din da aka kai a wani gidan jarida a babban birnin tarayyar Nijeriya, Abuja ya hallaka mutane 3, a sa’ilinda wata fashewar kuma daura da ofishin jaridar a birnin Kaduna da ke arewacin kasar ta hallaka akalla mutane 3.

Hukumomi sun ce fashewa ta farko a yau Alhamis ta auku ne a ofishin jaridar This Day da ke birnin Abuja, wanda daya ne daga cikin manyan jaridun Nijeriya. Wani mazaunin wurin ya gaya wa Muryar Amurka cewa fashewar ta girgiza gidanda da misalign karfe 11 a.m. agogon wurin.

Ciyaman din kwamitin tsare-tsaren rubutun jaridar, Olusegun Adeniya, ya ce wani dan kunar bakin wake ne ya abka ta mashigar ginin da wata mota samfurin jeeb. Ya ce harin ya yi sanadin kashe wasu masu gadi biyu da maharin.

A halin da ake ciki kuma, wani wakilin Muryar Amurka ya fadi a Kaduna cewa ‘yan sanda na rike da wani wanda ake zargi bayan da bam ya tashi da kusan karfe 12 na rana agogon wurin daura da wani ginin da ya kunshi ofishin jaridar ta This Day da wasu jaridun kuma biyu – “The Moment” da kuma “The Sun.” Hukumomi sun ce fashewar ta yi sanadin mutuwar mutane 3 tare da raunata wasu da dama.

Wani mazaunin garin Kaduna Diji Obadiah ya ce maharin ya abka wa ginin da ya kunshi ofishin jaridar da motarsa, a daidai lokacin da ya ke ta cewa “Allahu alkbar.”

Obadiah ya ce mutane sun so su kashi maharin da duka bayan da ya dauko wani bam daga cikin motarsa ya jefa kan cincirindon jama’a.

Nan take dai babu wanda ya dau alhakin kai harin.

XS
SM
MD
LG