Wani dake ikirarin shine kakakin Boko Haram yace kungiyar ta yanke duk wani tsaida shawarwari da gwamnatin Najeriya.
Wani mutum da ya kira kansa Abul Qaqa, ya fada jiya talata a birnin Maiduguri cewa, kungiyar ta fara shawarwari ta bayan fage da gwamnati, amma yanzu shawarwarin ya wargaje.
Kamar yadda kakakin yake cewa “mun rufe duk wasu kofofin shawarwari. Ba zamu sake sauraron wani kira na shiga shawarwari ba. Jami’an tsaro suyi duk abinda suke jin zasu iya yi, mu kuma zamu yi amfani da duk abinda muka mallaka domin yin abinda zamu iya ……”.
Kalaman sunzo ne kwanaki kacal bayanda wani shehin malami Dr. Ahmed Datti, ya bada sanarwar ya janye daga shiga tsakani. Yace bai yarda da gwamnati ba saboda an fallasa batun shawarwarin da ake yi a asirce.
An fara shawarwarin ne da nufin kawo karshen watanni da aka dauka kungiyar tana kai hare hare galibi a arewacin Najeriya. Ana azawa kungiyar laifin kashe daruruwan mutane cikin sekara daya da rabi data shige.
Shugaba Goodluck Jonathan yana fuskantar karin matsin lamba ya maido da zaman lafiya a arewacin Najeriya. Galibin hare haren kungiyar tana auna su ne kan ‘Yansanda, jami’an gwamnati da wasu shugabannin jama’a.
A kokarin shawo kan rikicin ne cikin ‘yan watannin baya bayan nan, Mr. Jonathan ya ayyana dokar ta baci cikin kananan hukumomi 15, ya kuma tura karin sojoji zuwa arewacin kasar, duk da haka ana ci gaba da fuskantar hare hare daga kungiyar.
Babu cikakken bayani kan wan nan kungiya, duk da haka an hakikance tana son shimfida tsarin shari’a.
Duniya ta sami labarin kungiyar ce a karo na farko a 2009, lokacin da suka tada wani mummunan rikici kan gwamnati. Gwamnati tayi amfani da karfin soja mai tsanani wajen murkushe boren bayan fada da aka gwabza na mako daya, har aka kashe kimanin mutane 700.