Shugaban Amurka Barack Obama yace hukumomin Amurka sun bankado “wani shirin ta’addanci” da aka kitsa kan Amurka, bayan an gano wani kunshi da ake shakka,cikin jirgin dakon kaya zuwa Amurka.
Jami’ai sun hakikance kwalayen reshen kungiyar al-Qaida dake Yemen ce ta tura.
Da yake magana a fadar White Jumma’an nan,shugaba Obama yace kwalayen guda biyu duka,da aka kama daga ketare,an aika su ne ga wasu wuraren ibadar yahudawa a Chicago.
Shugaban yace Amurka zata ci gaba da hada kai da gwanatin kasar Yemen domin wargaza reshen kungiyar al-Qaida dake kasar.
Haka kuma shugaba Obama yace hukumomin yaki da ta’addanci zasu dauki dukkan matakai da suka wajaba domin kare lafiyar Amurkawa.
Tunda farko a yinin Jumma’a,hukumomi a Amurka,da Ingila,da gabas ta tsakiya sun dauki karinmatakan tsaro a tashar jirage da inda jiragen dakonkaya ke lodi,bayan gano wadan nan kunshe kunshe da ake shakkar abinda ke ciki,kan hanyarsu ta zuwa Amurka.