A yau alhamis shugabannin Kungiyar Tarayyar Turai zasu gana a Brussels domin tattauna hanyoyin rigakafin matsalolin kudi da zasu iya jefa tattalin arzikin kasashe 27 na tarayyar cikin hatsarin rushewa.
Ana sa ran shugabar gwamnatin kasar Jamus, Angela Merkel, da shugaba Nicolas Sarkozy na Faransa zasu yi kiran da a yi garambawul ga yarjejeniyar da ta tabbatar da kafuwar tarayyar da ta fara aiki a watan Disamba a bayan tattaunawar shekara da shekaru.
A makon da ya shige shugabannin biyu suka yarda zasu nemi da a yi gyara ga Yarjejeniyar Lisbon domin ta kunshi tanadi na yadda za a magance rikicin kudi tare da yanke hukumcin da za a yi ma kasashen da suke da wagegen gibi a kasafce-kasafcen kudinsu. Irin wannan hukumci zai hada da dakatar da ikon irin wadannan kasashe na jefa kuri’a.
Amma shugabannin Tarayyar Turai da dama su na yin adawa da duk wani yunkurin sauya yarjejeniyar, matakin da zai bukaci amincewar dukkan kasashe 27 na wannan kungiya.