Tsohuwar ‘yar takarar mataimakiyar shugaban kasa karkashin inuwar jam’iyyar Republican, kuma ‘yar lelen gungun Tea Party ta masu tsananin ra’ayin rikau, Sarah Palin, ta ce zata tsaya takarar shugaban kasa idan har aka rasa wanda zai yi.
Palin ta fada cikin wani shirin telebijin mai suna “Entertainment Tonight” cewa tilas dan takara ya kasance mai ra’ayin rikau na zahiri, mai rajin kare tsarin mulki, kuma wanda zai iya yanke shawara komai dacinta ba tare da damuwar irin sukar da zai iya sha ba.
Amma kuma, ko da ta yanke shawarar tsayawa takarar ma, Palin zata fuskanci kalubale sosai. Kuri’un neman ra’ayoyin jama’a na baya bayan nan sun nuna tana bayan sauran ‘yan jam’iyyar Republican wadanda watakila zasu yi takara, yayin da wasu kuri’un neman ra’ayoyin suka nuna cewa shugaba Barack Obama zai doke ta da gagarumin rinjaye a zaben shugaban kasa na 2012.
Haka kuma a jiya alhamis, wani kakakin tsohon shugaba Bill Clinton yace Mr. Clinton yayi kokarin neman dan Democrat Kendrick Meek da ya janye daga takarar sanata na tarayya daga Jihar Florida. Kakakin yace da farko Meek ya yarda, amma daga baya sai ya canja ra’ayi.
Dan takarar jam’iyyar Republican Marco Rubio da dan indipenda Charlie Crist sun ba Meek rata mai yawa a kuri’un neman ra’ayoyin jama’a. Kakakin na Clinton yace tsohon shugaban yayi imani da cewa idan Meek ya janye, dan Indipenda Crist zai samu karin kuri’u har ya iya kada dan jam’iyyar Republican Rubio.