Tarihi ya nuna cewa jam’iyyar dake rike da fadar White House a nan Amurka, tana shan kashi a babban zaben farko na ‘yan majalisa a tsakiyar wa’adin sabon shugaba, kuma a yau talata din ma, kuri’un neman ra’ayoyin jama’a da kuma masu fashin bakin siyasa sun nuna cewa hakan ake kyautata zaton zai faru.
A zahiri, wasu masu fashin bakin siyasar da ake girmamawa sun yi hasashen cewa ‘yan jam’iyyar Republican su na iya samun karin kujeru fiye da hamsin a majalisar wakilan tarayya dake hannun ‘yan Democrat a yanzu. Wannan kuwa ya zarce adadin kujeru 39 da suke bukata domin kwace wannan majalisa ta wakilan tarayya.
Ana takarar dukkan kujeru 435 na majalisar wakilan, amma kwararru sun ce kimanin kashi daya cikin hudu ne kawai ake gwagwagwa a kansu.
A majalisar dattijai ma, ana sa ran ‘yan jam’iyyar Republican zasu samu karin kujeru, amma akasarin kwararru sun ce zai yi wuya su samu kujeru 10 da suke bukata kari domin kwace majalisar. A bana, ana takarar kujeru 37 ne daga cikin kujeru 100 na majalisar dattijan.
Shugabannin jam’iyyun biyu sun yi ta kai gwauro da mari domin zaburar da magoya bayansu, ciki har da shugaba Barack Obama wanda ya hau durom a Jiharsa ta Illinois, inda yake cewa "Idan dukkan wadanda suka yi yakin wanzar da sauyi a 2008 zasu fito a bana, zamu lashe wannan zabe na 2010."
‘Yan Republican su na sa ran cin moriyar kuri’un neman ra’ayoyin jama’a dake nuna cewa Amurkawa sun damu da tattalin arziki da rashin aiki, kuma su na son ganin an samu sauyi a majalisar dokoki. Tsohon dan majalisar wakilan tarayya dan jam’iyyar Republican, Dick Armey, ya shafe shekara guda da ta shige yana kyamfe ma gungun ‘yan tsananin ra’ayin rikau da ake kira ‘yan Tea Party, bangaren dake sa ran fito da jama’a masu dan karen yawa domin zaben ‘yan jam’iyyar Republican a yau. Dick Armey ya ce, "Jam’iyyar Republican ta koyi darasi cikin shekara gudan da ta shige, ta fara kasa kunne tana sauraren Amurkawa. Wannan shi ya sa jam’iyyar zata lashe zaben yau."
‘Yan jam’iyyar Democrat sun kwace majalisar dokoki daga hannun ‘yan Republican a zaben tsakiyar wa’adi na biyu na shugaba George W. Bush a shekarar 2006, suka kuma kara yawan rinjayen kujerunsu a zaben 2008 lokacin da Mr. Obama ya zamo shugaban kasa. Amma kuma, shaihin malamin siyasa na Jami’ar Virginia, Larry Sabato yace rashin ingantuwar tattalin arziki a cikin gida ya bude kofa ta kwace majalisar dokoki ga ‘yan jam’iyyar Republican a wannan shekarar.
Zaben yau talata zai yi tasiri sosai kan yadda shugaba Obama zai kammala shekaru biyun da suka rage masa kan kujera. Idan ‘yan Republican suka kwace majalisa guda ko duka biyu, zasu samu saukin toshe kafar zartas da manufofin shugaban na cikin gida, kuma zasu samu karin tasiri a manufofin hulda da kasashen waje ciki harda yakin Afghanistan.
A bayan wadannan zabubbuka na majalisar wakilai da ta dattijai, za a gudanar da zaben gwamnoni a jihohi 37 daga cikin 50 na nan Amurka. A nan ma, kwararru su na hasashen cewa za a samu sabbin gwamnoni ‘yan jam’iyyar Republican.